

- Yadda yan IPOB suka kashe ‘yan Arewa 10 ciki har da mace mai juna biyu da ‘ya’yanta 4 da wasu mutane 6 a jihar Anambra - May 24, 2022
- Sama da mutane 30 ne aka ruwaito sun bace a jihar Borno bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai musu hari - May 24, 2022
- Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya karbi tikitin takarar Sanatan Gombe ta Arewa domin tsayawa takara a jam’iyyar PDP a 2023 - May 24, 2022
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jiya yace Najeriya na bisa turbar samun wadatar abinci. Ya danganta hakan da shirin bayar da lamuni ga manoma na babban bankin kasa (CBN).
Shugaban Kasar ya sanar da haka a Abuja yayin da yake kaddamar da dalar shinkafa ta babban birnin tarayya.
Hakan na zuwa ne daidai lokacin da gwamnan babban bankin kasa (CBN) Godwin Emefiele yace ya zuwa yanzu gwamnatin tarayya ta zuba naira tiriliyan 1 wajen samar da shinkafa a cikin kasa.
Shugaban kasar ya bayyana samun karuwar shinkafar da ake nomawa da sarrafawa a cikin kasa da cewa tabbacine na samun wadatar abinci nan gaba.
Ya kara da cewa za a kara samun yawaitar shinkafar idan sabbin kamfanonin sarrafa shinkafa guda 2 sun fara aiki a jihoshin Lagos da Katsina.
Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar da takwaransa na jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu, na daga cikin manyan bakin da suka halarci bikin.