Mai martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussain Adamu ya bayar da tabbacin masarautarsa na wajan bayar da cikakken hadin kai da goyan baya wajen samun nasarar aikin kidayar al’umma da ake sa ran gudanarwa a bana.

Sarkin ya bayar da tabbacin ne a jiya, lokacin da kwamishinan hukumar kidaya na kasa a jihar Jigawa Garba AG Zakar ya ziyarci fadarsa dake Kazaure.

Alhaji Najib Hussain Adamu ya bayyana muhimmancin da aikin kidayar yake dashi ga alumma da cigaban kasa.

Sarkin ya bukaci jama a da su marawa hukumar baya wajen samun saukin gudanar da aiyukan hukumar.

A jawabinsa kwamishinan hukumar Alhaji Zakar yace ana sa ran gudanar da aikin kidayar ne a watan Mayun bana inda ya nemi hadin kai da goyan bayan sarakuna a matsayinsu na iyayen kasa wajen samun nasarar aikin kidayar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: