Kwamatin hukumar tsara tattalin arziki na jihar Jigawa ya fara rangadin duba ayyuka

0 65

Kwamatin hukumar tsara tattalin arziki na jihar Jigawa ya fara rangadin duba ayyukan hadin gwiwa da na mazabu a shiyyar Jigawa ta tsakiya.

A jawabinsa, a sakateriyar karamar hukumar Dutse, kwamishinan kudi na jiha, Babangida Umar Gantsa, ya ce kwamatin zai duba ayyukan mazabu da kuma ayyukan hadin gwiwa na jiha da kananan hukumomi da aka bayar a shiyyar Jigawa ta tsakiya a tsakanin shekara ta 2020 zuwa yanzu.

Ya ce an kafa hukumar tsara tattalin arziki ta jihar Jigawa ne domin inganta ayyukan da aka gudanar tare da samar da isassun kudaden gudanar da ayyukan da kuma samar da kyakkyawan tsari na aiwatar da ayyukan ga al’umma.

A jawabinsa shugaban karamar hukumar Dutse, Bala Usman Chamo ya yabawa Gwamna Muhammad Badaru Abubakar bisa aiwatar da ayyukan raya kasa masu amfani ga al’ummar jihar Jigawa.

Ya bayar da tabbacin bayar da dukkanin tallafin da kwamitin ke bukata domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: