

- Gwamna Zulum ya raba wa likitoci fiye da 80 didaje da kudi Naira miliyan 79 don inganta rayuwarsu - July 2, 2022
- Manyan Sarakunan kasar Yarabawa sunyi kiran samun zaman lafiya daga gwamnati kafin zaben 2023 - July 2, 2022
- Kasar Jamus za ta fara dawo wa da Najeriya dubban kayayyakin tarihin ta da aka wawushe tun lokacin mulkin mallaka - July 2, 2022
Wasu ‘yan bindiga a dajin Gando da ke karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara sun rubutawa wasu mutanen kauyuka 9 takardar neman kudi ko kuma su fuskanci munanan hare-hare.
Wannan dai na zuwa ne ‘yan makonni bayan da ‘yan bindiga suka kashe akalla mutane 200 a kananan hukumomin Bukkuyum da Anka.
A wannan kashe-kashe, ‘yan bindigar sun kone kauyuka biyar, da kashe mazauna da dama tare da lalata gawarwakinsu.
Mazauna kauyukan sun shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar da suka kai farmaki kauyukan a kan babura sama da 500.
Wasikun da Editan mu ya gani an rubuta da harshen Hausa kuma an rubuta su ne zuwa ga kauyuka daban-daban.
Kowace wasika na dauke da sunan kauye a sama da kuma adadin kudi da za’a biya.
Akwai kuma lambar wayar hannu da aka rubuta akan wasikun.
Dukkanin wasikun sun kunshi bayani iri daya in ban da sunan garin da adadin kudin da ‘yan fashin dajin ke nema.