kasar Mali ta zargi Faransa da goyawa shugabannin juyin mulki baya

0 84

Ministan Harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop, ya cewa matsalar dangantakar dake tsakanin su da Faransa ta biyo bayan nisanta da manufofin kasar ne, sabanin jinkirta zaben shugaban kasar kamar yadda aka takura musu suyi.

Ministan, ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi ga Yan kasar Mali mazauna Brussels, inda ya zargi Faransa da nuna son kai wajen kalubalantar mulkin soji.

Faransa wadda tace ke kare mulkin dimokiradiya taje wasu kasashe inda ta dora shugabanni da suka yi juyin mulkin na soji ta kuma jinjina musu. inji ”ministan”.

Dangantaka tsakanin Mali da Faransa wadda ta yiwa kasar mulkin mallaka tayi kamari tun bayan juyin mulkin da soji suka yi a watan Agustan shekarar 2020.

Faransa na da dubban sojoji a kasar Mali wadanda ke rundunar yaki da Yan ta’adda a yankin Sahel.

Ana ci gaba da cece-kuce a kasar tun bayan takunkumin da kungiyar kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS ta dorawa Mali na karya tattalin arziki sakamakon juyin mulkin wanda ya samu goyan bayan Faransa da Amurka da kungiyar kasashen Turai.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian ya bayyana gwamnatin sojin Mali a matsayin haramtacciya, inda ya zarge ta da kaucewa gudanar da zabe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: