Masu zanga-zanga sun kawo wa zaman kotu cikas yayin da take ƙoƙarin ci gaba da sauraron ƙarar Mu’azu Magaji (Win Win) kan zargin cin zarafin Gwamna Ganduje da iyalansa.

Wakilin BBC a Kano ya ambato jami’an kotun da ke Nomans Land, Sabon Gari a Kano na cewa ba za su fara sauraron ƙarar ba har sai ‘yan zanga-zangar sun bar wurin.

Matasa ɗauke da kwalaye da ke nuna goyon baya ga tsohon kwamashinan na ayyuka sun yi cincirundo a bakin kotun, yayin da wasu ɗalibai kuma ke kiran da a hukunta shi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: