Kashim Shettima Ya Bude Sabbin Gidajen Alkalan Babbar Kotun Tarayya A Abuja

0 202

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ƙaddamar da sabbin gidaje guda 10 da aka gina domin manyan alkalan Babbar Kotun Tarayya (Federal High Court) a Gundumar Katampe da ke Abuja, tare da miƙa musu mukullan gidajen.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda Shettima ya wakilta, ya bayyana cewa walwala da jin daɗin alkalai na da muhimmanci wajen tabbatar da ‘yancin kai da ingancin bangaren shari’a.

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ne ya jagoranci aikin gina gidajen, inda ya ce an yi hakan ne domin ƙarfafa tsarin shari’a da samar wa alkalai muhalli mai kyau da kwanciyar hankali.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan ƙaddamar da makamantan gidaje guda 10 na alkalan Kotun Ɗaukaka Ƙara (Court of Appeal), yayin da gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a kuma gina irin waɗannan gidaje ga alkalan Babbar Kotun Abuja (FCT High Court), Kotun Masana’antu ta Ƙasa (National Industrial Court) da kuma jami’an Code of Conduct Tribunal.

Leave a Reply