Kashim Shettima ya nemi dalibai su rugumi ilimin da suke da shi domin bada gudunmawa a Najeriya

0 142

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya nemi daliban kasar nan sun rugumi ilimi da suke da shi domin bada gudunmawa wajen cigaban kasar nan, a maimakon lalubo hanyoyin cigaban kasar nan.

Kashim Shettima ya nemi wannan bukata ne yayinda shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa kuma tsohon kakakin Majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya jagoranci daliban da suka samu daraja ta daya data biyu a shirin karbar horo kan shugabanci, yayinda suka kai masa ziyara a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Mataimakin shugaban kasar ya nemi daliban da suka halarci wannan shirin da suyi watsi da duk wani nau’I na jiran tsammani suyi amfani da basisar da suke da ita domin cigaban kasar nan.

Kazalika, ya nemi wadanda suka halarci shirin da su samun horo kan sanin makamar shugabanci da su kasance ana damawa da su domin samun nasarar cigaban kasar nan. Da yake jawabi wadanda ya assasa shirin Hon. Gbajabiamila yace, ya shirya shirin domin cigaban mutane maza da mata ‘Yan Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: