Shugaba Tinibu ya nemi Majalisar Dattawa ta tabbatar da alkalan Kotun Koli 11

0 180

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinibu ya nemi Majalisar Dattawa ta tabbatar da alkalan Kotun Koli 11.

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio shine ya sanar da wasikar shugaban kasa a zaman majalisar na yau.

Kwamitin alkalai da harkokin shari’a na Majalisar Dattawan ya fara tantance alkalan 11 da majalisar kolin shari’a ta kasa ta aike da sunayen su.

Daga cikin su akwi mai shari’a Haruna Tsammani wanda ya jagoranci shari’ar kararar shugaban kasa na 2023. Bayan tabbatar da Alkalan, Kotun kolin na da alkalai 21 kamar yadda kundin tsarin kasa ya sahale.

Leave a Reply

%d bloggers like this: