An amince da da fitar da kudi kimanin Naira Bilyan 6 domin gina rukunin gidaje 1,500 a jihar Jigawa

0 158

Majalisar zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da fitar da kudi kimanin Naira Bilyan 6 domin gina rukunin gidaje 1,500 da nufin rage karancin gidaje a Jihar Jigawa.

Kwamishinan yada labarai, Matasa,Wasanni da al’adu na jihar Jigawa Sagir Musa shine ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse.

Sagir Musa yace gidajen da za’a gina sun kunshi gidaje masu dakuna uku-uku a ciki, da gidaje masu dakuna biyu-biyu sare a wasu sassana Jihar nan.

Yace wannan aiki yayi dai-dai da manufofin 12 na gwamnatin Gwamana Malam Umar Namadi domin ‘Yan jihar jigawa su samu saukin rayuwa.

Kwamishinan yace tuni aka fitar da kudi kimanin Naira Bilyan 5.9 domin fara aikin.

Ya kara da cewa za’a gina rukunin gidaje 600 a babban Birnin Jiha Dutse,da rukunin gidaje 200 a Hadejia da 100 a Kazaure sai kuma kananan hukumomin Gumel, Ringim da Birnin-Kudu. Yace za’a gina gidajen guda 150-150 a kananan hukumomin Babura da Kafin-Hausa da nufin magance karancin muhalli a jihar Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: