Katunan Shaidar Zama Ɗan Ƙasa 4,000 Sunyi Kwantai A Jigawa

0 131

Hukumar shaidar zama dan kasa tace akwai katinan shaidar zama dan kasa guda 4,000 da masu su basu karba ba a jihar Jigawa.

Jagoran hukumar anan jihar, Mallam Aminu Jakada, shine ya bayyana haka yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Kasa a Dutse.

Aminu Jakada wanda ya bayyana hakan a matsayin abu mai karya gwiwa, ya bukaci masu katunan, musamman daga yankunan Kananan Hukumomin Hadejia da Kirikasamma da Gumel, da su ziyarci ofisoshin hukumar na kananan hukumominsu dan su karba.

Yace manufar samar da katin shine bawa masu katinan damar su mallakin katin shaidar zama dan kasa, tare da yin amfani da number shaidar zama dan kasa, wajen gujewa jin kunya a harkokinsu nan gaba.

Jagoran sai yayi nuni da cewa, number shaidar dan kasa na aiki, kuma da ita ake tantance sahihancin bayanan kowane mutum a ma’adabar bayanan hukumar.

Aminu Jakada sai kuma ya shawarci masu neman katin da su ziyarci ofishin hukumar dake kusa da su, domin samun kati da number shaidar zama dan kasa.A cewarsa, hukumar na da wajen yin rijistar katin sama da 40 a fadin jiarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: