Kenya ta yi watsi da sukar da Amurka ta yi mata kan China

0 101

Majalisar Dokokin Kenya ta yi watsi da sukar da Majalisar dokokin Amurka ta yi mata akan alaƙarta da ƙasar Sin, wanda ke nufin tana ci gaba da ja baya daga dangantakarta da Washington.

Shugaban kwamtin tsaro da harhohin ƙasashen waje na Kenya Nelson Koech dai ya ce ƙasarsa na da cikakken ‘yancin yin hulɗa da kowace ƙasa a duniya a ɓangarori da dama musamman na tallin arziki.

“Kenya na neman haɗaka da sassan duniya, daga ciki Afirka na bayar da gagarumar gudummuwa ga ɓangarorin da suka shafi ci gaban duniya da tattalin arziki. Wannan ya nuna manufar gwamnatin shugaba Trump na fiito da sabbin tsare-tsare da suka shafi cibiyoyi da ƙasashen duniya,” in ji Nelson Koech.

Wannan sabuwar jayayyar dai ta soma ne bayan da shugaban kwamtin hulɗa da ƙasashen waje na majalisar dokokin Amurka, Jim Risch ya gargaɗi Kenya akan abin da ya kira alaƙa mai “illa” tsakanin ta da China, bayan da shugaban ƙasar Kenya William Ruto ya goyi baya tare da neman a samar da gamayya ɗaya da za ta haɗa kan duniya wadda kuma China za ta jagoracin samar da ita.

Ruto ya bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kai China a watan Afirilu.

Leave a Reply