Kimanin Dabbobi dubu 7,718 aka yiwa rigakafin cutukan dabbobi a karamar Hukumar Hadejia.

Jamiin kula da cutukan dabbobi na yankin Zakar Usman Beita ya sanar da hakan a lokacin da ya ziyarci shugaban karamar Hukumar Alhaji Bala TO

Yace an yi rigakafin ne kyauta domin kare dabbobi daga kamuwa daga cutukan dabbobi

Zakar Usman ya kara da cewar daga cikin dabbobi da aka yiwa rigakafin sun hadar da shanu 3,278 da awaki da tumaki 4,236 da kuma karnuka 36

Yace an raba maganin dabbobi na dubban naira a asibitocin kula da dabbobi yayinda aka yi amfani da tawaga uku wajen samun nasarar hujjin dabbobi na bana a fadin yankin

A jawabinsa shugaban KH Alhaji Bala TO ya yaba da wannan ziyara da kuma nasarar da aka samu wajen hujjin dabbobin na bana tare da godewa kungiyoyin Fulani da manoma bisa hadin kan da suka bayar wajen samun nasarar rigakafin

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: