Gwamnatin tarayya ta ce dole ne a yiwa duk wani Ma’aikacin gwamnati rigakafin cutar Corona.

Sakataren Gwamnatin tarayya Boss Mustapha Gida, shine ya bayyana hakan, inda ya ce duk ma’aikacin da ya ki karbar rigakafin za’a hanashi zuwa wurin aiki.

Boss Mustapha Gida, wanda shine shugaban Kwamatin Shugaban Kasa kan yaki da cutar Corona, ya fadi hakan ne a lokacin da yake yiwa manema labarai karin haske a jiya.

A cewarsa, daga ranar 1 ga watan Disamba, duk Ma’aikacin da yaki nuna katin shaidar anyi masa rigakafin cutar Corona, zai bar ofishin gwamnati da yake aiki a ciki.

Shugaban Kwamatin, ya ce kididdigar da suke samu, ta yi nuni da cewa cikin makonni 4 da suka gabata, an samu raguwar yaduwar cutar a wasu jihohi.

Haka kuma ya ce gwamnatin tarayya ta cire takunkumin da ta kakabawa kasashen Afrika da Kudu da Turkiya da kuma Brazil na hana zuwa kasashe.

Kazalika, ya ce Kwamatin zai sake yin Nazari kan matakan da kasashen duniya, da kuma hukumomin lafiya suke dauka kan yaduwar cutar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: