Wani Dan Majalisar wakilai Hon Fakeye Olufemi, ya bayyana bukatar a kakaba dokar biyan kudin haraji ga masu Kananan Sana’oi ciki harda Kafintoci, da Direbobin motocin haya.

Mista Olufemi, wanda shine dan Majalisar tarayya mai wakiltar Boluwaduro/Ifedayo/Ila na Jam’iyar APC daga Jihar Osun ya bayyana hakan ne a zaman majalisar na jiya Laraba.

Dokar biyan kudaden haraji ta shekarar 2020, ta cire masu Kananan Masana’antu wanda jarinsu bai kai Naira Miliyan 25 ba, daga cikin masu biyan haraji.

A cewar Mista Olufemi, kakabawa masu Kananan masana’antu su rika biyan kudaden haraji zai ragewa gwamnati nauye-nauyen, tare da bunkasa samun kudaden harajin ta.

Haka kuma ya ce kaso 80 zuwa 90 na yan Najeriya suna aikin dogaro da kansu ne, kuma basa biyan kudaden haraji.

Kazalika, ya ce kawo sauye-sauyen zai taimakawa gwamnati wajen ganin cewa kowanne dan Najeriya yana bada gudunmawarsa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: