Wasu da ake kyautata zaton yan bindiga ne sun kashe sojoji 5 a kauyen Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Garin Wanzamai na da nisan kilomita 60 tsaninsa da birni Gusau na jihar kuma maharan sun jima suna addabar yankin.

Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai na Jihar Alhaji Ibrahim Dosara, shine ya tabbatar da hakan ga BBC Hausa, sai dai bai bayyana adadin sojojin da suka mutu ba.

Rahotanni na cewa sojojin sun kai dauki garin ne a lokacin da aka kira su a waya, inda yan bindigar suka bude musu wuta a kan hanyar su ta zuwa garin.

Mazauna yankin sun ce an tsayar da zirga-zirgar ababen hawa a hanyar Gusau zuwa Funtua mai nisan kilomita 100.

Sama da wata daya Kenan da katse sadarwa a wasu yankunan jihar Zamfara tare da rufe kasuwannin mako-mako a wani bangare na tsaurara matakan yaki da yan bindiga.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: