Cibiyar Dakile yaduwar cututtuka ta Kasa NCDC ta ce kimanin mutane 251 ne suka harbu da cutar Corona a kasar nan baki daya cikin awanni 24 da suka gabata.

Cibiyar ta ce mutanen da suka harbu da cutar sun fito ne daga jihohi 13 na kasar nan ciki harda babban birnin tarayya Abuja.

NCDC ta ce birnin tarayya Abuja shine yake da mutane 78 da suka harbu da cutar sai Lagos mai 46.

Sauran Jihohin da aka samu bullar cutar sun hada da Kaduna (27), Rivers (21), Imo (16), Edo (13), Delta (12), Plateau (10), Niger (7) Bauchi (6), Kwara (6), Akwa Ibom (4), Benue (3) and Nasarawa (2).

Anyi nasarar sallamar mutane 187 bayan sun warke daga cutar, sai dai kuma a gefe guda ta hallaka mutane 5 a jiyan.

Kawo yanzu, kimanin mutane dubu 2,761 ne cutar ta hallaka a kasar nan.

Kazalika, tun bayan bayyana cutar a kasar nan kimanin mutane dubu 208,404 ne suka harbu da cutar, inda aka yi nasarar samun mutane dubu 196,123 da suka warke daga cutar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: