Rundunar Yan sandan Jihar Jigawa sun kama wani Dan shekara 31 mai suna Abdullahi Maikudi, bisa zargin sa da laifin damfara masu hulda da bankuna a birnin Dutse.

Kakakin rundunar ASP Lawan Shiisu Adam, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

A cewarsa, sunyi nasarar kama mutanen ne bayan wasu mutane 2 sun gabatar da korafin su cewa mutumin ya cucesu bayan sunje cire kudaden su a Na’urar ATM dake Dutse.

ASP Lawan Shiisu Adam, ya ce mutumin da ake zargin ya cuci mutanen ne ta hanyar sauya mutu katinan su na cirar kudade, inda ya cire Naira dubu 50,000 a Asusun mutum 1, inda kuma ya cire Naira dubu 8,000 a Asusun daya mutumin da shima ya yaudara.

Kakakin Yan sandan ya ce bayan kama mutumin ya basu bayanan sirri inda suka yi nasarar kama wani abokin aikin sa mai suna Surajo Habibu Limawa, na karamar hukumar Dutse. Kazalika, ya ce suna cigaba da bincikar mutanen kafin su gabatar dasu a gaban Kotu. 

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: