Labarai

Ma’aikatar lafiya ta Jihar Jigawa ta ce ta horas da jami’an kiwon lafiyar hanyoyin kariya daga cututtukan da suke halaka kananan yara

Ma’aikatar lafiya ta Jihar Jigawa ta ce ta horas da jami’an kiwon lafiya hanyoyin kariya daga cututtukan da suke halaka kananan yara a kokarinta na samar da yara masu koshin lafiya.

Daraktan kiwon lafiyar al’umma na ma’aikatar, Dakta Abdullahi Umar Namadi ya bayyana haka a wurin bude taron bitar masu ruwa da tsaki na yini biyu kan dabarun shawo kan cutar sanyi a jihar Jigawa wadda ake gudanarwa a cibiyar horas da ma’aikata ta jiha dake birninDutse.

Dakta Abdullahi Umar Namadi ya yi kira ga mahalarta taron bitar su tattaunawa kana su fito da barun da zasu magance matsalolin ciwon sanyi a jihar nan.

A nasa jawabin Mista Ayenouwo Olanrewaju na ma’aikatar lafiya ta tarayya ya bayyana cutar sanyi ta Pneumonia a matsayin cuta mai jawo illa ga kananan yara da mutuwarsu a kasar nan.

An zabo mahalarta taron ne daga kafofin yada labarai da kungiyoyin kyautatuwar zaman jama’a da hukumomin hadin gwiwa da kuma hukumomin gwamnati.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: