Kungiyoyin Masu Ruwa da Tsaki na Jam’iyar APC ta Jihar Kano sun rubuta korafin ga uwar Jam’iya ta kasa domin kawo musu dauki kan abinda yake faruwa a rikicin siyasar jihar.

Gamayyar kungiyoyin sun rubuta korafin nasu ne ga Shugabancin Jam’iyar na Rikon Kwarya a matakin Kasa, kan kokarin kakaba musu shugabancin Jam’iyar a matakin Jiha.

Cikin mutanen da suka rubuta korafin sun hada da Sanata Ibrahim Shekarau, Sanata Barau Jibrin Maliya da sauran dan majalisar wakilai, kamar yadda manema labarai suka samu kofin takardar korafin.

Masu korafin sunyi watsi da zaben shugabannin Jam’iyar na Matakin Mazabu da kuma Kananan Hukumomi wanda aka gudanar a jihar.

Kazalika, masu korafin sun ce basu amince da zaben shugabannin Jam’iyar da aka gudanar a jihar ba, biyo bayan yadda aka sabawa wasu dokokin Jam’iyar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: