Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa an kashe masallata 10 a harin da aka kai wani masallaci a yankin Tillaberi da ke Yammaci a Laraba.

Yan bindigar sun kai harin a Abankor, kauyen da ya hada kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso.

Wani ganau ya bayyana wa jaridar AFP cewa ” maharan sun isa kauyen a kan babura ana tsakiyar Sallar Magriba suka bude wa masallata wuta.”

Tun farkon shekaran ne hare-hare ke dada karuwa a yankin Tillaberi musamman kan iyakar yankin da makwabtan kasashe.

Ko a farkon wata Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa kusan mutane 600,000 da ke zaune a yankin Tillaberi na fuskantar bala’in karancin abinci.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: