Jam’iyar APC ta goyi bayan kudurin Majalisar dattawa na gudanar da zabukan Jam’iyu na cikin gida ta hanyar yin kato bayan kato.

Jam’iyar ta nanata kudurin na goyan bayan tsarin ta yadda hakan zai sake inganta tsarin zabe da kuma karfafa demokradiya.

Sakataren Jam’iyar na Kasa Sanata John James Akpanu, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, inda ya ce ya kamata ayi watsin da bukatar PDP na soke kudurin.

Jam’iyar APC ta ce Majalisar ta cancanci yabo, biyo baya irin namijin kokarin da tayi wajen tabbatar da hakan.

Kazalika, ta ce hakan yana cikin kudurin gwamnatin shugaban Kasa Muhammadu Buhari na tabbatar da cewa an sake karfafa demokradiya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: