Kimanin kaso 20 cikin 100 na kudaden da jihar Jigawa take tarawa tayi asarar sa saboda cutar Corona

0 66

Hukumar Tattara Kudaden Harajin Cikin Gida ta Jihar Jigawa ta ce kimanin kaso 20 cikin 100 na kudaden da take tarawa ne tayi asarar sa saboda cutar Corona.

Shugaban Hukumar Alhaji Ibrahim Ahmed Muhammad, shine ya bayyana hakan ga manema labarai a Ofishin sa, bayan ya karbi bakuncin Hukumar hadin gwiwa kan harkokin tara kudaden shiga ta kasa.

A cewarsa, Cutar Corona wanda ta daidaita tattalin arzikin Kasashen Duniya, ta kawo cikas kan kudaden Harajin da Gwamnatin Jihar Jigawa take samu.

Haka kuma ya ce hukumar tana kokari wajen ganin ta cike gibin da ta samu, tare da sake inganta hanyoyin karbar kudaden.

A Jawabinta, Sakatariyar Hukumar hadin gwiwa kan harkokin tara kudaden shiga ta kasa wanda Hajiya Aisha Ribadu ta wakilta, ta ce sun kawo ziyara jihar nan ne domin tallafawa hukumar tara kudaden shiga ta jiha domin samun nasarar cimma manufofin da ta sanya a gaba.

Haka kuma, ta yabawa Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, bisa sanya hannu kan Dokokin hukumar Haraji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: