Shugaba Buhari ya nuna alhininsa ga Gwamnatin Kasar Jamhuriyar Nijar, biyo bayan iftila’in ambaliyar ruwa a kasar

0 76

Shugaban Kasa Muhari Buhari ya nuna Alhininsa ga Gwamnatin Kasar Jamhuriyar Nijar, biyo bayan iftila’in da ya faru na ambaliyar ruwa a kasar.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja, inda ya bayyana faruwar lamarin a matsayin abin takaici da Kaduwa.

Sanarwar ta ce Shugaban Buhari, ya jajantawa Shugaba Bazoum Muhammad, da Gwamnatin Kasar Nijar, bisa faruwar lamarin wanda ya janyo asarar rayuka da rushewar gidaje.

A cewar Garba Shehu, shugaban Buhari ya ce abinda ya faru a cikin kwanaki biyu a Jamhuriyar Nijar abin tausayawa ne, inda ya jajantawa gwamnatin kasar.

Kazalika ya ce kasashen Duniya ciki harda Nijar suna cigaba da fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a wannan shekara, kuma suna kokarin dakile matsalar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: