Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 120 a karamar hukumar Guri

0 70

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 120 a unguwar tsallake dake garin Guri, hedilwatar karamar hukumar Guri.

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Musa Shu`aibu Muhammad wanda ya bayyana haka ga Manema Labarai yace mutane da dama sun rasa mahallinsu sakamakon ambaliyar.

Alhaji Musa Shu`aibu Muhammad wanda ya jajantawa wadanda ambaliyar ta shafa, ya bukaci hukumar bada agajin gaggawa ta jiha ta kai musu dauki, inda yace karamar hukumar ta raba fatun buhuna domin yin jinga, baya ga cire chiyawar kachalla.

Shugaban karamar hukumar wanda ya bukaci hukumar bada agajin gaggawa ta jiha ta kai musu dauki, ya shawarci al`ummar yankin su guji shan-gurbatccen ruwa domin kare kansu daga cututtuka.

Yace tuni karamar hukumar ta kashe naira dubu dari hudu wajen sayo magunguna wanda aka rabawa mutane a garuruwa bakwai inda cutar tayi kamari.

Yace nan bada jimawa karamar hukumar zata sayo kayayyakin abinci da na amfanin yau da kullum domin rabawa wadanda iftila`in cutar amai da gudawa ta rutsa da su a yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: