Yara biyar sun mutu bayan wani Gurneti da suke wasa da shi ya tarawatse a Jihar Borno

0 65

Akalla yara biyar sun mutu bayan wani Gurneti da suke wasa da shi ya tarawatse a garin Ngala na Jihar Borno.

Lamarin dai ya faru ne ranar Alhamis a garin da ke dab da kan iyakar Najeriya da kasar Kamaru, kamar yadda wani dan sa-kai a yankin ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP.

Wani Dan Sakai mai suna Umar Kachalla ya ce Yaran su biyar sun dauko Gurnetin ne lokacin da suke kiwo a wajen garin, inda ya fashe a hannunsu, lokacin da suke wasa da shi.

Ya ce Biyu daga cikinsu sun mutu ne nan take, ragowar ukun kuma sun mutu a asibitin Mada, da ke kasar Kamaru.

Kazalika, shi ma wani dan aikin sa-kan, Umar Ari ya bayar da makamancin wannan bayanin inda ya ce lamarin ya faru ne ranar Alhamis.

Malam Umar Ari ya ce har yanzu burbushin Gurneti na ci gaba da yin barna a yankin, musamman a kan yara kanana wadanda ko dai suke mutuwa ko kuma su jikkata.

A watan Agustan 2014, mayakan kungiyar Boko Haram sun taba kwace iko da garin na Ngala da na Gambori da ke da makwabtaka da shi.

Mazauna yankunan dai sun yi zargin cewa ’yan ta’addan Boko Haram ne suke ba yaran kyautar Gurnetin a matsayin kayan wasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: