Kimanin mambobin kungiyar Boko Haram 10 ne suka mika wuya ga sojojin Najeriya da suke jihar Borno

0 63

Kimanin Mambobin Kungiyar Boko Haram 10 ne suka mika wuya ga Sojojin Najeriya da suke Jihar Borno, kamar yadda wata Majiya daga Sojojin ta fadawa manema labarai.

Baya ga mayakan kungiyar Boko Haram 10 da suka mika wuya, akwai Yara 5 da suka mika wuya ga sojojin.

Wata Majiya ta fadawa manema labarai cewa mayakan sun fito ne daga yankunan Jango da Mandara cikin karamar hukumar Gwoza ta Jihar.

An bayar da rahotan cewa Mayakan sun mika wuya ne ga rundunar Soja ta 151 wanda ta yi sansani a Banki da ke karamar hukumar Bama a jiya Lahadai.

Manema labarai sun rawaito cewa Mambobin Kungiyar ta Boko Haram da suka mika wuya, suna karkashin Jagorancin Bijirarren Shugaban Kungiyar Bakura Salaba, wanda aka kashe kwanan nan.

Kwamandan Rundunar Operation Hadin Kai Christopher Musa, ya ce kawo yanzu Mayakan Boko Haram dubu 11 da 349 da Matan su dubu 15 da 289 da kuma Yayan su dubu 24 da 163 ne suka mika wuya ga Sojojin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: