Kimanin mutane 22 ne suka mutu a wani hadarin mota da ya afku a gabashin Tanzania

0 92

Kimanin mutane 22 ne suka mutu a wani hadarin Mota da ya afku a gabashin Tanzania, a cewar fadar shugaban Kasar.

Fadar Shugaban Kasar cikin wata sanarwa ta kuma ce hadarin ya raunata mutane 38.

Shugaban yan sandan yankin Gabashin Morogoro, Mista Fortunatus Muslim, ya ce lamarin ya faru ne a yankin Melela Kibaoni, wanda ya ke da nisan Kilomita 200 daga birnin Dar es Salaam, babbar birnin kasar ta Tanzania.

A cewarsa, babbar motar ce ta bar hanyar ta inda ta daki wata karamar Mota.

Shugabar Kasar ta Tanzania Samia Suluhu Hassan, a sakon da ta wallafa a shafin ta na Twitter ta bayyana damuwar ta kan faruwar lamarin, inda ta bukaci masu ababen hawa su rika bin ka’idojin tuki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: