Shugaban Sojojin Najeriya Laftanar Janar Farouk Yahaya, a jiya ya bayyana cewa Sojoji baza su bar rigima ta Dabayyaye zaben da ke tafe a shekarar 2023 ba.

Shugaban ya bayyana hakan ne a taron da Sojojin suka gudanar a watanni 3 na shekarar 2022 da muke ciki kan ayyukan su.

A cewarsa, Sojojin zasu cigaba da samar da yanayi mai kyau ta yadda za’a gudanar da zabe cikin nasara ba tare da firgita fararen hula ba.

Farouk Yahaya, ya umarci Jami’an su kasance masu gudanar da ayyukan su cikin kwarewa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar domin samar da tsaro a ciki da wajen kasa.

Haka kuma, ya bukaci su cigaba da gudanar da ayyukan su kamar yadda suka dauki rantsuwa a lokacin da aka kaddamar da su.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: