Wani Matashi mai suna Rabiu Musa dan shekara 32 ya gamu da ajalin sa a Jihar Kano bayan gini mai hawa uku ya rufta dashi akan hanyar Ahmadu Bello Way.

Kakakin hukumar kashe gobara na Jihar Kano Saminu Abdullahi, shine ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kano, inda ya ce ginin da ya rufto din ana kan aikin sa ne, a lokacin da ya danne mutum 2.

Ginin ya rufe wani mutum mai suna Danjuma Tijjani mai shekaru 52 sai dai an ceto shi a cikin buraguzan ginin.

Sanarwar ta ce Marigayi Rabiu Musa ya rasu ne sakamakon munanan raunikan da ya ji.

Haka kuma kakakin hukumar kashe gobarar ya ce an garzaya da mutanen biyu zuwa babban Asibitin Kwantarwa na Muhammad Abdullahi Wasai, domin samun kulawa sai dai likitoci sun tabbatar da mutuwar Musa Rabiu a can.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: