Majalisar Wakilai ta bayyana damuwa bisa yadda ake samun karuwar yaran da basa zuwa makaranta wanda adadin su ya kai Miliyan 10 da dubu 500

0 51

Kakakin Majalisar Wakilai Hon Femi Gbajabiamila, ya bayyana damuwa bisa yadda ake samun rahotannin karuwar yaran da basa zuwa Makaranta wanda adadin su ya kai Miliyan 10 da dubu 500.

Kakakin Majalisar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar Yara 500 da aka sanya a makaranta, tare da aikin Ido kyauta ga mutane dubu 10,000 wanda aka aiwatar a Jihar Zamfara.

Mista Femi wanda ya samu wakilcin Shugaban Ma’aikatan Ofishin sa, Malam Garba Rikiji, ya bayyana damuwa bisa yadda ake samun karuwar yaran da basa zuwa makaranta a kasar nan.

Haka kuma ya bukaci shugabannin da sauran kungiyoyin Al’umma su hada hannu wuri guda domin magance matsalar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: