Cibiyar NCDC tace mutum 122 ne suka rasa rayuwarsu a sakamakon kamuwa da zazzabin lassa a 2022

0 105

Cibiyar dakile bazuwar cutuka ta kasa NCDC  yace mutane 122 ne suka rasa rayuwarsu a sakamakon kamuwa da zazzabin lassa a shekarar 2022 da muke ciki.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani rahoto data wallafa kan illar da zazzabin yayi wa kasarnan daga ranar 7 ga watan da muke ciki zuwa ranar 13 ga watan Maris.

Rahoto  cutar na makon daya gabata ya bayyana cewa, muane 57 ne suka rasu a mako na 9 inda mutane 33 sukayi saura.

An rawaito cewa jihohin da aka samu mutuwar mutanen a makon daya gabata sun hada jihar Edo, Ondo, Ebonyi, Kogi, Gombe, Nasarawa, Taraba, Bauchi da jihar Kebbi.

A cewar rahotan, tun farkon shekarar nan Kimanin mutane dubu 3, 79 akayi zargin sun kamu da cutar a fadin kasar nan, wanda aka tabbatar da mutane 630 da suke dauke da cutar.

Jumillar jamia’an lafiya 45 kuma aka tabbatar sun kamu da cutar tsakanin watan Junairu daya gabata zuwa watan Maris da muke ciki.

Rahotan ya ce a shekarar 2022, jihohin kasar nan 23 akalla an samu mutum guda daya harbu da cutar a kananan hakumomi 87 da ke fadin jihohin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: