Kimanin mutane 36 sun sake kamuwa da cutar corona a Najeriya

0 105

Cibiyar dakile yaduwar cuttutuka ta kasa NCDC ta ce, kimanin mutane 36 ne suka kamu da cutar corona a Jihohin kasar nan 4 ciki harda babban birnin tarayya Abuja.

Wannan Alkaluman da hukumar ta fitar a yammacin jiya, ya kara yawan mutane da suka kamu da wannan cutar zuwa dubu 253,727 tin bayan bullarta a 2020.

NCDC ta kuma ce a jiyan ba’asamu asarar rayauka ba, hakanne ya tabbatar da cewa kimanin mutane dubu 3,139 ne wannan cutar ta hallaka a fadin kasar nan tin bayan bullarta.

An kuma sallami mutane dubu 230,045 bayan sun warke daga wannan cutar.

Alkaluman na jiya ya nuna cewa jihar Legas wacca itace tafi yawan wadanda suka kamu da wannan cutar, a jiyan ansamu mutane 23.

Sai babban birnin tarayya Abuja da mutane 5 sai kuma Osun da mutane 4.

Amma a jiyan ba’asamu ko mutum daya ba, daya kamu da wannan cutar a jihar Nasarawa ba, duk da yawan mutanen dake kamuwa da wannan cutar a kwanan nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: