Gwamnatin jihar jigawa ta bada kwangilar hanyar zagaye wato bye pass a cikin garin Hadejia.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya sanar da hakannne a jiya Lahadi a garin Hadejia a wajen bikin karramawar da kungiyar Hadejia Ina Mafuta ta shirya masa a kofar fada dake cikin garin Hadejia.

Ya kuma ce nan bada jimawa dan kwangilar zai kai kayayyakin aiki domin fara aikin hanyar gadan gadan.

Gwamna Badaru Abubakar ya kuma nanata kudirin gwamnatinsa na cigaba da aiwatar da aiyukan raya kasa domin cimma Muradin alummar jihar nan.

Ya kuma godewa kungiyar bisa shirya bikin domin nuna kokarin sa, wajan aiwatar da aiyukan raya kasa ga alummar jihar nan baki daya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: