‘Kisan gillar da ake yiwa mutane na ne yasa na shiga yin fashin daji’ Bello Turji

0 127

Shahararren Dan Fashin Dajin nan Bello Turji, ya bayyana dalilan da suka sanya ya zama daya daga cikin Rikakkun yan fashin Daji da suke addabar Arewacin Najeriya.

Bello Turji, ya yi kaurin suna wajen farmakar Arewacin Kasar nan fiye da shekaru, tare da kashe Dubban mutane, da kuma sace Dalilan Makarantu samu da 10 cikin shekara 1.

Manema Labarai sun rawaito cewa biyo bayan hare-haren Bello Turji, Dubban Kauyawa ne suka yi sansani a wuraren daban-daban, ya yinda wasu kuma suka samu mafaka a Jamhuriyar Nijar, biyo bayan gazawar gwamnati wajen basu kayan Jinkai.

Da yake zantawa da Manema Labarai, Bello Turji, ya ce ya shiga aikin fashin Daji ne biyo bayan yankan ragon da ake yiwa mutanan sa a Kasuwar Shinkafi.

Bello Turji, ya karyata labaran da ke cewa yana da Alkala da yan Kungiyar Boko Haram, inda ya ce basu da Alaka da Siyasa.

Kazalika, ya caccaki Matasan Yan Sakai, biyo bayan yadda suke hada hannu da Jami’an tsaro wajen Firgita Fulani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: