Kwalejin Ilmi da Nazarin Sharia ta garin Ringim ta samu sahalewar gwamnatin jiha na fara karatun digiri a wasu bangarori

0 67

Kwalejin Ilmi da Nazarin Sharia ta garin Ringim ta samu sahalewar gwamnatin jiha na fara karatun digiri a wasu bangarori.

Shugaban kwalejin Dr Suleiman Haruna ya sanar da hakan a lokacin babban taron shekara shekara karo na uku da kungiyar malamai ta kwalejin ta shirya.

Yace kwalejin ta samu amincwar fara karatun digiri a bangaren Arabia da Turanci da Hausa da Tarihi da addinin musulunci da kuma ilmin firamare.

Dr Suleiman Haruna ya kara da cewar gwamnatin jiha ta gina sabbin ajujuwan koyar da dalibai guda uku da kammala dakin lacca mai daukar kujeru 250.

Ya yi kira ga gwamnatin jiha data duba matsalolin da kwalejin take fuskanta da suka hadar da karancin malamai da sauran maaikata da kuma karancin ofisoshi da kayayyakin dakin karatu.

A jawabinsa shugaban taro Dr Abbas Abubakar Abbas ya yi kira ga masu ruwa da tsaki dasu hada hannu wuri guda domin ceto halin da ilmi yake ciki domin tallafawa rayuwar matasa masu tasowa.

A jawabinsa shugaban kungiyar malamai na kwalejin Comrade Auwal Haruna yace ana gudanar da taron ne domin lalubo matsalolin dake damun kasa da hanyoyin magancesu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: