Kofin Duniya 2026: Masu Horaswa Shida Sun Rasa Aikinsu Bayan Ficewa Daga Gasar

0 49

Kofin Duniya 2026: Masu Horaswa Shida Sun Rasa Aikinsu Bayan Ficewa Daga Gasar

Kocin tawagar ƙasar Jamus, Julian Nagelsmann, ya zama koci na shida da ya rasa aikinsa bayan ficewar ƙasarsa daga Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026.

Jamus ta kasa tsallakawa zuwa zagayen ‘yan 16 bayan da Paraguay ta doke ta a wasan zagaye na 32.

Bayan wannan rashin nasara, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Jamus (DFB) ta sanar a hukumance cewa Nagelsmann ya yi murabus daga muƙaminsa na kocin ƙungiyar ƙasa.

Da haka ne Nagelsmann ya shiga jerin kociyoyin da suka rasa aikinsu bayan ficewar ƙasashensu daga gasar, waɗanda suka haɗa da Sebastián Beccacece na Ecuador, Ronald Koeman na Netherlands, Miroslav Koubek na Czechia, Steve Clarke na Scotland da Hong Myung-bo na Koriya ta Kudu.

Da yake jawabi bayan murabus ɗinsa, Nagelsmann ya ce yana matuƙar baƙin cikin rashin samun nasarar faranta wa magoya bayan Jamus rai a gasar.

Ya ce, “Ina matuƙar baƙin ciki saboda ban iya ba wa magoya baya lokutan farin ciki a Kofin Duniya ba, kuma ban cika abin da suka sa ran gani daga gare ni ba.”

Rahotanni sun ce Nagelsmann ya bayyana wa manyan jami’an DFB a wata ganawa ta sirri cewa yana son sauka daga muƙaminsa bayan ficewar Jamus daga gasar da Amurka, Kanada da Mexico suka karɓi baƙunci.

Nagelsmann mai shekara 38 ya karɓi ragamar horar da Jamus a watan Satumban 2023, inda ya jagoranci ƙasar zuwa zagayen kwata fainal na gasar Euro 2024 kafin Spain ta fitar da ita daga gasar.

Leave a Reply