Kotu a Jamhuriyar Nijar ta yanke hukunci a kan ƙarar lauyoyin dangin Mohammed Bazoum

0 198

Wata kotu a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar ta yanke hukunci a kan ƙarar lauyoyin dangin hamɓararren shugaban ƙasa Mohammed Bazoum, waɗanda aka kama, kuma ake tsare da su.

Ana zarginsu ne da hannu a yunƙurin Bazoum na tserewa daga inda shugaban mulkin sojin ƙasar, Abdourahamane Tchiani ke tsare da shi.

Kotun ta ce kama mutanen da tsare su, ba sa kan ƙa’ida, don haka ta umurci hukumomin mulkin sojin Nijar, su saki mutanen nan take.

Ta kuma ce gwamnatin Nijar za ta biya tarar CFA miliyan ɗaya ga duk wuni ɗaya da za su sake yi a hannun hukuma. Sojojin fadar shugaban ƙasa ne suka kama mutanen a wani samame da suka kai wani gida cikin birnin Yamai ranar da aka zargi Bazoum da yunƙurin tserewa zuwa Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: