Gwamnatin jihar Filato zata biya wa musulmi yan asalin jihar guda 500 kudin aikin hajjin bana

0 151

Gwamnatin jihar Filato tayi alkawarin daukar nauyin biyan kudin aikin hajjin bana ga musulmi yan asalin jihar dari biyar.

Wannan dai na kunshe ta cikin wata takardar sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Jama’atu Nasrul Islam ta kasa reshen jihar, Sarkin Wase Muhammad Sambo na uku.

Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin buda baki da gwamnan jihar Caleb Mutfwang, ya shirya a fadar gwamnatin jihar.

Shugaban kungiyar ta Jama’atul Nasrul Islam ta kasa reshen jihar ta Filato, ya godewa gwamnan bisa wannan karamci da ya nuna musu don kai ziyara zuwa kasa mai tsarki. Mai martaba Muhammad Sambo, ya yi kira ga daukacin al’ummar musulmi dake zaune a jihar da su marawa kudurin gwamnati a kokarin ta na kawo cigaban a fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: