

- Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC - May 27, 2022
- Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya - May 27, 2022
- Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa - May 27, 2022
Wata babbar kotu dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta warware dokar da ta bada umarnin dakatar da babban taron jam’iyyar APC na kasa da zai gudana karshen watan da muke ciki.
Jam’iyyar APC mai mulki ta sanya ranar 26 ga watan Maris da muke ciki domin gudanar da babban taron.
Mai shari’a Bello Kawu, a ranar 18 ga Nuwamba, 2021, ya bayar da umarnin dakatar da taron har zuwa wani lokaci bayan Mista Salisu Umoru, ya kai jam’iyyar Mai Mala Buni da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a gaban kotu don kalubalantar babban taron da aka shirya yi.
A yan makonnin nan dai an samu tirjiya ta cikin gida kan babban taron.
Da yake zartar da hakuncin mai sharia Kawu yace kotun bata da wata kwakkwarar hujjar dakatar da babban taron.
Kotun ta warware hakuncin ranar 18 ga watan nuwambar 2021, da zai dakatar da babban taron.
Daga nan ya dage sauraron karar zuwa ranar 30 ga Maris don sauraren karar.