Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke wadda ta umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta soke rajistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyu huɗu.
Kotun ta umarci INEC da kada ta ɗauki wani mataki na soke rajistar jam’iyyun har sai an kammala sauraron ƙarar da suka shigar kan hukuncin da kotun ƙasa ta yanke.
Tun da farko, Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya ya umarci INEC ta soke rajistar ADC da Accord Party da wasu jam’iyyu uku bisa zargin kasa cika sharuɗan da kundin tsarin mulki ya tanada.
Da yake yanke hukuncin a ranar Litinin, Mai Shari’a Peter Lifu ya ce jam’iyyun ba su samu kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da doka ta tanada a zaɓukan da suka gabata ba.
Jam’iyyun da hukuncin ya shafa sun haɗa da African Democratic Congress (ADC), Accord (A), Action Alliance (AA), Action Peoples Party (APP) da Zenith Labour Party (ZLP).
Sai dai kwamitin alƙalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara ya soki yadda aka yanke hukuncin, yana mai cewa an yi watsi da ikon da kotun take da shi.