Kudurin neman kafa dokar yin gwaji domin gano yiwuwar haihuwar mai cutar sikila wato Genotype da ciwon hanta ya samu karatu na farko

0 120

Kudurin neman kafa dokar yin gwaji domin gano yiwuwar haihuwar mai cutar sikila wato Genotype da ciwon hanta wato Hepatitis ya samu karatu na daya a zauren majalisar dokokin jihar Jigawa.

Wakilin mazabar Babura a majalisar dokokin, Alhaji Kabiru Isah, ya gabatar da wannan kuduri da nufin samar da dokar yin gwaji a tsakanin ma’aurata da nufin shawo kan karuwar haihuwa masu dauke da ciwon sikila.

Sakamakon rashin daidaiton kwayar halitta a tsakanin ango da amarya da kuma yawaitar masu dauke da ciwon hanta.

Shugaban majalisar, Alhaji Idris Garba Jahun, ya umarci akawun majalisar, Barrister Musa Aliyu Abubakar, ya yi karatu na daya akan kudurin yayin da ‘yan majalisar za su yi muhawara nan gaba akan wannan batu.

Daga nan aka dage zaman majalisar zuwa ranar Talata ta makon gobe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: