Kwanaki biyu bayan da ‘yan bindiga suka kashe ‘yan sa kai 63, ‘yan bindigar sun sake kashe jami’an tsaro 19

0 208

Kwanaki biyu bayan da ‘yan bindiga suka kashe ‘yan sa kai 63, ‘yan bindigar sun sake kashe jami’an tsaro 19 a cikin tawagar mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Samaila Yombe, a kauyen Kanya da ke karamar hukumar Danko Wasagu ta jihar.

Lamarin na baya-bayan nan ya faru ne a ziyarar da mataimakin gwamnan ya kai yankunan jihar da hare-haren ‘yan bindigar ya shafa.

Majiyoyi da dama sun ce ‘yan bindigar sun auka wa mataimakin gwamnan, Samaila Yombe, wanda dan asalin garin Dabai ne a karamar hukumar Zuru.

Mataimakin gwamnan ya tabbatarwa da BBC Hausa a yammacin jiya cewa yana kauyen lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari.

Wani dan karamar hukumar Danko Wasagu, Labaran Magaji, ya shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen Kanya da misalin karfe 5 na yamma.

A cewar Labaran Magaji, an kashe sojoji 13 da jami’an ‘yan sanda shida da ke tare da ayarin mataimakin gwamnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: