Kungiyar dalibai ta kasa ‘yan asalin jihar Jigawa (NAJISS) ta gabatar da fakiti 700 na audugar mata da kwalaye 10 na garin sabulu

0 76

Kungiyar dalibai ta kasa ‘yan asalin jihar Jigawa (NAJISS) ta gabatar da fakiti 700 na audugar mata da kwalaye 10 na garin sabulu da sinadarin hypo ga daliban makarantar Arabiyya ta gwamnati ta ’yan mata dake Babura.

Mataimakin shugaban kungiyar Kwamared Ali Mati ne ya bayyana haka a lokacin da yake mika kayan ga hukumar makarantar.

Ya ce kungiyar ta shirya shirin wayar da kan al’umma kan kiwon lafiya da tsaftar jiki tare da duba lafiyar daliban jiharnan.

Kwamared Ali Mati ya kuma ce kungiyar ta samu damar duba yadda makarantar ke gudanar da ayyukanta a dakin dafa abinci da ajujuwa a makarantar.

Mataimakin shugaban kungiyar ta NAJISS ya yabawa babban sakataren ma’aikar lafiya Dr Salisu Muazu, da na ma’aikatar ayyuka Injiniya Datti Ahmed, bisa goyon baya da hadin kai domin samun nasarar shirye-shiryen kungiyar NAJISS.

Leave a Reply

%d bloggers like this: