Biyo bayan kashe ‘yan sa kai 63 da ‘yan bindiga suka yi a jihar Kebbi, majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tura jami’an soji

0 87

Biyo bayan kashe ‘yan sa kai 63 da ‘yan bindiga suka yi a jihar Kebbi, majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tura jami’an soji zuwa kananan hukumomin da abin ya shafa.

Haka kuma ta bukaci sojojin da su kafa sansanin soji guda biyu a kananan hukumomin Yauri da Sakaba na jihar.

‘Yan majalisar sun bukaci gwamnatin tarayya da ta kafa dokar ta-baci kan harkokin tsaro a yankin Arewa maso Yamma da sauran sassan Najeriya da abin ya shafa.

Kiran ya biyo bayan kudirin da Tanko Sununu na jam’iyyar APC daga jihar Kebbi da sauran ‘yan majalisa bakwai daga jihar Kebbi suka gabatar a jiya.

Da yake gabatar da kudirin, Tanko Sununu ya ce shekaru kadan baya jihar Kebbi ta kasance daya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya.

Ya ce an kyale ‘yan bindiga suna cin karensu babu babbaka a jihar Kebbi saboda jami’an tsaro a jihar ba su da kayan aikin da za su iya magance su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: