Kungiyar IPOB ta sanar da aniyarta ta dakatar da dukkan harkokin rayuwa a yankin Kudu saboda tsare Nnamdi Kanu
Kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biafra ta sanar da aniyarta ta dakatar da dukkan harkokin rayuwa a yankin Kudu maso gabashin Najeriya saboda ci gaba da tsare shugabanta Nnamdi Kanu.
A wata sanarwa da Chika Edoziem, wanda ya bayyana kansa a matsayin mai rike da mukamin shugaban sashen gudanarwa na kungiyar ya sanya wa hannu, IPOB ta ce ta ba gwamnatin Najeriya kwana 11 ta saki Nnamdi kanu domin kaucewa killace yankin.
Edoziem ya fitar wannan gargadin ne kwana biyu bayan da wasu da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar ta IPOB ne su ka kashe wani babban jami’in ‘yan sanda mai mukamin DPO a jihar Imo.
Mista kanu dai ya tsere ne bayan da wata kotu ta bayar da belinsa a shekarar 2017.