

- Yadda yan IPOB suka kashe ‘yan Arewa 10 ciki har da mace mai juna biyu da ‘ya’yanta 4 da wasu mutane 6 a jihar Anambra - May 24, 2022
- Sama da mutane 30 ne aka ruwaito sun bace a jihar Borno bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai musu hari - May 24, 2022
- Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya karbi tikitin takarar Sanatan Gombe ta Arewa domin tsayawa takara a jam’iyyar PDP a 2023 - May 24, 2022
Hukumar ayyukan ruwan Najeriya (NIHSA) ta yi hasashen cewa tsakanin watan Agusta da farkon Oktoba, za’ayi mumunan ambaliyan ruwan sama a Najeriya.
NIHSA tace ambaliyar zata munana a wasu jihohi da birnin tarayya Abuja.
Dirakta Janar na hukumar, Injiniya Nze Clement Onyeaso, a hirar da yayi da manema labarai a Abuja, ya ce dukkan jihohin da aka ambata a farkon shekara zasu fuskanci ambaliya su shirya.
Ya yi kira ga yan Najeriya su shiryawa wannan ambaliya ta hanyar gyara magudanun ruwa tare da cire bola, ciyayi, gansakuka dss.
A watan Mayu, anyi hasashen mumunan ambaliyar ruwan sama a jihohin Najeriya akalla 28 a bana, sabon rahoton hasashen ambaliya AFO ya nuna. Ana fitar da wannan rahoto ne a kowani shekara.
Jihohin da aka lissafo sune,Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, FCT, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano and Kebbi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba da Zamfara.
Ministan arzikin ruwa, Suleiman Adamu, ya lissafa wadannan jihohi ne ranar Alhamis a taron gabatar da rahoton hasashen ambaliya na shekara-shekara na hukumar ayyukan ruwa a Najeriya (NIHSA).