Kwamitin Takarar Shugaba Tinubu Karo Na Biyu Ya Ziyarci Jihohin Bayelsa Da Enugu

0 154

Kwamitin Tabbatar da Amincewar Sake Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa na Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara jihohin Bayelsa da Enugu domin ci gaba da tattara sa hannun gwamnoni a kan fom ɗin amincewa da takararsa.

A ziyarar da aka gudanar ranar Laraba, 24 ga Yuni, 2026, tawagar ƙarƙashin jagorancin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Ibrahim Kabir Masari, ta samu rakiyar wasu manyan jami’an gwamnati da magoya baya.

A jihohin biyu, gwamnan Bayelsa, Douye Diri, da gwamnan Enugu, Peter Mbah, sun tarbi tawagar tare da sanya hannu a fom ɗin amincewar, a wani ɓangare na shirin neman goyon bayan gwamnoni ga sake tsayawar Shugaba Tinubu.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnonin Adamawa da Delta suka sanya hannu a irin wannan fom a ranar Talata, a ci gaba da gangamin neman amincewar gwamnoni kafin zaɓen 2027.

Leave a Reply