Kwanturola Janar na Hukumar Shige da Fice ta Kasa, Muhammad Babandede ya yi ritaya

0 305

Kwanturola Janar na Hukumar Shige da Fice ta Kasa, Alhaji Muhammad Babandede, ya yi ritaya bayan ya shafe shekaru 36 yana aiki a hukumar.

Mataimakin Babban Kwanturola Janar mai kula da harkokin kudi, Idris Isah Jere, zai fara aiki a matsayin mukaddashin shugaban hukumar har zuwa lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai nada wani Kwanturola Janar na hukumar.

Muhammad Babandede, wanda aka nada Kwanturola Janar na Hukumar Shige da Fice ta Kasa a ranar 15 ga Mayu 2016, ya karbi ragamar mulki daga hannun Martin Kure Abeshi.

Ya gabatar da sauye-sauye masu yawa a hukumar da suka hada da mayar da ayyukan hukumar zuwa na komfuta da samar da fasfo daga waje daya ta internet, da bai wa baki Visa idan sun iso kasarnan, da sauransu.

Kwanturola Janar mai ritaya, wanda ya yi alkawarin zama jakadan Hukumar ta Kula da Shige da Fice, ya ce a ko da yaushe zai kasance a shirye domin ya bayar da gudunmawa a duk lokacin da hukumar ta nemi hakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: