Kotun daukaka kara ta dakatar da gwamnatocin Ribas da Legas daga karbar harajin kayyaki na VAT

0 150

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta dakatar da gwamnatocin jihohin Ribas da Legas daga karbar harajin kayyaki na VAT.

A hukuncin da ya yanke a yau, Mai Shari’a Haruna Simon Tsanami, ya kuma bayar da umarnin a dakatar da dokar da Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta zartar kuma Gwamna Nyesom Ezenwo Wike ya amince da ita.

Alkalin ya zartar da hukuncin ne sa’o’i kadan kafin Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos ya rattaba hannu kan dokar harajin VAT. Gwamna Sanwo-Olu ya rattaba hannu kan dokar ne jim kadan bayan ya isa jiharsa daga Abuja.

Hukuncin kotun daukaka kara ya biyo bayan bukatar da hukumar tattara kudaden shiga ta tarayya ta nema na dakatar da aiwatar da umurnin wata babbar kotun jihar Ribas a kan lamarin.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas, a watan Agusta ta tabbatar da ikon jihar na karbar harajin kayayyaki na VAT da na kudaden da daidaikun mutane ke samu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: